<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ina son Mai Ceto, Yesu,
 Ƙaunarsa ce zancena,
 Ina murna domin giciyen,
 Can ya kau da laifina.

[V2]
 KORUS
 Ina waƙar Almasihu,
 Jininsa ne fansata,
 Tashinsa ne shaidar ceto,
 Babu sauran la'ana.

[V3]
 2) Ina cikin bautar Shaiɗan,
 Yesu ya ji tausayina,
 Sai ya zo ya ba da ransa,
 Yesu, ba mai kamarka.
 Korus

[V4]
 3) Ina ɗaukaka sunansa,
 Ƙarfin mutuwa ya ci,
 Har ya sa in yi tarayya
 Cikin nasara da shi.
 Korus

[V5]
 4) Ko a can a gunsa zaune,
 Ko a duniya saukakke,
 Kauna ce ta haɗa ranmu,
 Ni da Yesu ɗaya ne.
 Korus</lyrics>
<title>Ina Son Mai Ceto, Yesu LW296</title>
<hymn_number>296</hymn_number>
</song>